
Wata kungiya karkashin tsohon tsageran Naija Delta, Tampolo ta yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin kuri’u dubu 10 a zaben 2027.
Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar me suna Comrade Sunday Adekanbi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar ‘yancin Najeriya a Abuja inda ya jawo hankalin ‘yan Najeriya da su shiga kungiyar.
Yace a shekaru 2 da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi yana Mulki, ya dora Najeriya a Turbar ci gaban tattalin arziki.
Yace zasu yi aiki bisa jagorancin Tampolo dan tattaro kan ‘yan Najeriya su goyi bayan gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027.