
Tsohuwar Ministar sufurin jiragen sama, Stella Oduah ta amince zata mayar da Naira Biliyan 2.5 data sata.
Ta bayyana hakane a yayin zaman kotu a ranar Alhamis ita da wanda ake kararsu tare.
Tace maimakon ci gaba da shari’ar, ta amince ta mayar da udaden da ta sata.
Me kula da shari’ar, Rotimi Oyedepo ya tabbatar da cewa, Stella Oduah ta je ofishin babban lauyan Gwamnati kuma mw baiwa shugaban kasa shawara kan shari’a inda tace zata dawo da kudaden data sata.
Hakanan shima lauyanta, Onyechi Ikpeazu, SAN, ya tabbatar da hakan inda yace suna kan kokarin dawo da kudaden.
Lauyan dayan wanda ake zargi, Favour Osuanya shima yace du sun amince su mayar da kudaden.
Mai shari’a, Justice Hamza Muazu ya dage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Maris dan jin inda aka kwana kan maganar mayar da kudaden.