Wednesday, January 15
Shadow

Wani mutum da aka yi wa duka saboda zargin wulakanta Ƙur’ani a Pakistan ya rasu

Ƴansanda a Pakistan sun ce wani mutum Kirista da wasu Musulmi suka yi wa dukan tsiya, saboda zarginsa da saɓo, a watan da ya wuce ya rasu sakamakon raunukan da aka ji masa.

An kwantar da Nazir Masih, a asibiti a birnin Rawalpindi, bayan da gungun mutanen ya far masa tare da wasu a lardin Sargodha, bayan zarginsu da wulaƙanta Alƙur’ani.

Gungun mutanen ya kuma cinna wa wani gida wuta a lokacin harin.

An kama mutum ashirin da biyar kan zargin cewa suna da hannu a harin.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’Adam sun ce ana amfani da tsauraran dokokin Pakistan a kan laifukan saɓo ta hanyar da ba ta dace ba, domin biyan wasu buƙatu na ƙashin kai ko ramuwar gayya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo, yanda aka tursasa wani barawo cin Attarugu da Tafasashshen ruwan zafi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *