
Kungiyar ‘yan Kasuwar man fetur masu zaman Kansu PETROAN ta yi Allah wadai da rage farashin man fetur da Dangote yayi zuwa Naira 740 akan kowace lita.
Dangote ya rage farashinne daga yanzu har zuwa watan Fabrairu.
Inda ‘yan kasuwar suka ce hakan zai sa su rasa Kwastomominsu dakuma tafka asarar Naira Biliyan 100.
Kungiyar tace sabawa doka ne ace mutum daya ne zai rika kayyade farashin man fetur a Najeriya.
Tace a su kadai wannan lamari zai shafa ba haddashi Dangoten.