Wednesday, October 14
Shadow

Wannan Tsabar Muguntace, Inji Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu bayan da Dangote ya rage farashin man fetur dinsa zuwa Naira 740 aka kowace lita

Kungiyar ‘yan Kasuwar man fetur masu zaman Kansu PETROAN ta yi Allah wadai da rage farashin man fetur da Dangote yayi zuwa Naira 740 akan kowace lita.

Dangote ya rage farashinne daga yanzu har zuwa watan Fabrairu.

Inda ‘yan kasuwar suka ce hakan zai sa su rasa Kwastomominsu dakuma tafka asarar Naira Biliyan 100.

Kungiyar tace sabawa doka ne ace mutum daya ne zai rika kayyade farashin man fetur a Najeriya.

Tace a su kadai wannan lamari zai shafa ba haddashi Dangoten.

Karanta Wannan  Wani Malamin Addinin Islama daga kasar Yarbawa ya dauki hankula bayan da yace wai idan ka gayawa Saniya cewa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi Wafati zaka ga Bàlà'i, ba zaka koma gida Lafiya ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *