
Rahotanni sun bayyana cewa, Wasu Gwamnonin jam’iyyar APC na shirin komawa bangaren Atiku Abubakar saboda rikicinsu da Ministan Abuja, Nyesom Wike yaki karewa.
Rahoton yace Gwamnonin sun ce muddin Shugaban kasa da shugabancin jam’iyyar APC basu takawa Wike Birki ba a shishshigin da yake wajan zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
To lallai zasu goyawa Atiku Abubakar baya a zaben 2027.
Yusuf Musa wanda jigo ne a kungiyar dattawan Arewa ta ACF ne ya bayyana hakan ga jaridar TheWhistler.
Wike ya kawo wata kungiya me suna Rainbow wadda yake son duk wani me goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya shiga cikinta a yi masa yakin neman zaben 2027.
Saidai Gwamnonin APC sun ce ba zasu shiga wannan kungiya ba.