Friday, December 5
Shadow

Wata Sabuwa: An gano Makudan kudaden da shugaba Tinubu ya ware Kusa Tiriliyan 2 na gyaran Titunan Najeriya, Fiyade da rabin kudin Legas da kudancin Najeriya za’awa aiki dasu inda Arewa ta samu kaso kadan

A zaman majalisar Zartaswa na Ranar Litinin din data gabata, ta Amince da fitar da Naira Biliyan N787.14 da Dala Miliyan $651.7 dan yin gyaran Tutuna a fadin Najeriya.

Saidai binciken tsanaki da Dan Gidan Tanko Yakasai yayi ya nuna cewa Gaba dayan Dala miliyan $651.7, kusan Naira Tiriliyan daya duk Legas za’ kashewa.

Hakanan daga cikin Naira Biliyan N787.14 ita kuma Naira Biliyan N420Billion sama da kaso 50 cikin 100 na kudin kenan, Kudancin Najeriya za’a kashewa.

Hakan na nufin gaba daya baifi Naira Biliyan dari 3 bane za’a kashewa Arewa.

Karanta Wannan  Najeriya ta ƙara kuɗin yin fasfo

Dama dai a baya An so canja fasalin rabin kudin Haraji dan baiwa jihar data fi kawo kudi rabo me tsoka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *