Friday, December 5
Shadow

Wata Sabuwa, an shigar da karar neman tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu daga kan kujerarsa saboda cin zalin ‘yan kasa

Wani lauya me rajin kare hakkin al’umma, Mr. Olukoya Ogungbeje ya kai karar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda yace ya take hakkin ‘yan kasa.

Ya kai karar Tinubu ne babbar kotun tarayya dake Abuja inda yace Tinubun yana take hakkin ‘yan kasa da murkushesu a duk sanda suka yi yunkurin nuna rashin jin dadin mulkinsa ta hanyar zanga-zanga.

Ya kawo musalin Zanga-zangar da aka yi a watan Agusta na shekarar data gabata inda yace Gwamnatin Tinubu ta murkushe masu zanga-zangar da take hakkinsu na ‘yan kasa.

A cikin wadanda yake karar hadda babban lauyan Gwamati kuma Ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi inda yace yana neman kotu ta baiwa majalisar tarayya umarnin fara shirin tsigesu duka daga mukamansu saboda laifukan da suka aikata sun bada damar a tsigesu.

Karanta Wannan  'Yan Najeriya na son mu, ko bamu yi hadaka da kowace Jam'iyya ba zamu iya cin zaben 2027>>Inji Labour Party

Saidai lauyan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me suna Mr Sanusi Musa ya bayyana cewa Lauya Mr. Olukoya Ogungbeje baibi hanyar data kamata ba wajan shigar da karar, yace a bisa doka wanda aka takewa hakkinshi ne yake shigar da kara kotu, inda yace shi kuma Olukoya bai bayyana wani mutum guda da yake wakilta ba dake kukan an take masa hakkinsa.

Shima lauyan ministan shari’ar, Gbemga Oladimeji ya kalubalanci wannan kara inda yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a koda yaushe yana barin mutane suna bayyana ra’ayinsu ba tare da muzgunawa ba.

Alkalin kotun, Justice James Omotosho ya daga shari’ar zuwa 4 gawatan Maris.

Karanta Wannan  Facebook da Instagram sun kulle shafin mawakin Najeriya, Edris Abdulkarim saboda yiwa Trump waka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *