
Wata matashiya daga kasar Kenya ta kafa tarihin kasancewa wadda tafi kowa dadewa rungume da bishiya a Duniya, wannan bajinta tata tasa aka sakata cikin Kundin Tarihin Duniya.
Matashiyar me suna Truphena Muthoni ‘yar Kimanin shekaru 21 ‘yar Gwagwarmaya ce ta muhalli.
Ta yi wannan bajintace a wajan shakatawa dake Michuki Park a Birnin Nairobi na kasar ta Kenya.
Wakilin majalisar Dinkin Duniya bangaren Muhalli a kasar Kenya, Ababu Namwamba ya jinjinawa matashiyar kan wannan bajinta da ta yi.