Friday, February 7
Shadow

Kamar dai yanda suka rika fadi akan Tallafin Man Fetur, Gwamnatin tarayya tace wasu kalilanne ke amfana da tallafin wutar lantarki

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana biyan Naira Biliyan 200 a matsayin tallafin wutar lantarki duk wata.

Kuma tace wasu kalilanne da basu wuce kaso 25 cikin 100 na al’umma ba ke amfana da wananna tallafi inda tace talafin baya kaiwa ga wadanda ya kamata.

Babbar me baiwa shugaban kasa shawara akan makamashi, Olu Verheijen ce ta bayyana hakan a ranar Litinin.

Ta yi maganane akan rahoton dake cewa za’a kara farashin wutar lantarki da kaso 65 cikin 100.

Tace maganar da tayi ba’a fahimceta ba, tace abinda ta fada shine kudaden da ‘yan Najeriya ke biya na wutar lantarki suna biyan kaso 65 cikin 100 ne inda gwamnati ke biya musu sauran.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ganin kare yana cin Bulo ya baiwa mutane mamaki

Tace amma mafi yawa, masu kudi ne kalilan suka fi amfana da wannan tallafi na wutar lantarkin.

Game da karin kudin wuta da kuma zargin cewa wanda basu da mita suna biyan kudin wutar lantarkin da basu shaba, tace maganar gaskiya itace zasu kawo tsarin raba mita wanda za’a fara a wannan shekarar dan kawar da wannan matsala.

a lokacin da gwamnatin tarayya taso cire tallafin man fetur, ta rika yada cewa wasu kalilanne ke amfana da tallafin, saidai bayan da aka cireshi, kusan kowa ya ji a jikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *