Saturday, August 8
Shadow

Wata Sabuwa, an shigar da karar neman tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu daga kan kujerarsa saboda cin zalin ‘yan kasa

Wani lauya me rajin kare hakkin al’umma, Mr. Olukoya Ogungbeje ya kai karar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda yace ya take hakkin ‘yan kasa.

Ya kai karar Tinubu ne babbar kotun tarayya dake Abuja inda yace Tinubun yana take hakkin ‘yan kasa da murkushesu a duk sanda suka yi yunkurin nuna rashin jin dadin mulkinsa ta hanyar zanga-zanga.

Ya kawo musalin Zanga-zangar da aka yi a watan Agusta na shekarar data gabata inda yace Gwamnatin Tinubu ta murkushe masu zanga-zangar da take hakkinsu na ‘yan kasa.

A cikin wadanda yake karar hadda babban lauyan Gwamati kuma Ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi inda yace yana neman kotu ta baiwa majalisar tarayya umarnin fara shirin tsigesu duka daga mukamansu saboda laifukan da suka aikata sun bada damar a tsigesu.

Karanta Wannan  Akwai yiyuwar Tinubu ba zai so sauka daga Mulki ba, zai so ci gaba da zama shugaban Najeriya har karshen rayuwarsa>>Inji El-Rufai

Saidai lauyan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me suna Mr Sanusi Musa ya bayyana cewa Lauya Mr. Olukoya Ogungbeje baibi hanyar data kamata ba wajan shigar da karar, yace a bisa doka wanda aka takewa hakkinshi ne yake shigar da kara kotu, inda yace shi kuma Olukoya bai bayyana wani mutum guda da yake wakilta ba dake kukan an take masa hakkinsa.

Shima lauyan ministan shari’ar, Gbemga Oladimeji ya kalubalanci wannan kara inda yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a koda yaushe yana barin mutane suna bayyana ra’ayinsu ba tare da muzgunawa ba.

Alkalin kotun, Justice James Omotosho ya daga shari’ar zuwa 4 gawatan Maris.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Magidanci ya koka da cewa, matarsa ta bayar da gidansa jingina ta karbi bashin banki, a yanzu kuma bankin sun kwace gidansa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *