Wednesday, January 15
Shadow

WATA SABUWA: Harajin da ƴan Nijeriya ke biya ya yi kadan – Bill Gates

Senator Chris Coons meeting with Bill Gates at the Russell Senate Office Building on November 8, 2019.

Fitaccen Attajirin nan na duniya, Bill Gates wanda shi ne shugaban gidauniyar Bill da Melinda, ya ce harajin da ake karba a Nijeriya ya yi kadan.

Bill Gates ya yi bayanin hakan ne a taron tattaunawa na matasa kan samar da abinci mai gina jiki a Abuja a jiya Talata.

Majiyar mu ta Daily Nigerian Hausa daga Daily Trust ta rawaito cewa, Attajirin dan kasar Amurka yazo Nijeriya ne domin halartar taruka.

Da yake jawabi a taron, Bill Gates, ya ce karancin haraji da ake karba yana haifar da kalubalen kudi a fannin lafiya da ilimi.

Ya ce domin yan kasa su samu karfin gwiwa kan kokarin gwamnati na kula da lafiya dole ne a tabbata ana tafiyar da kudaden da ake warewa fannin lafiya a yadda ya dace.

Karanta Wannan  An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara

Bill Gates ya ce, ” Tsawon lokaci akwai shirye shirye ga Nijeriya wajen samar da kudade ga gwamnati fiye da yadda ake a yanzu. Abinda Nijeriya ke karba na haraji ya matukar kadan”, inji shi.

Me zaku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *