Wednesday, January 15
Shadow

WATA SABUWA: Laifi Mijin Hussaina Yayi, Afuwa Ya Kamata A Nema Masa, Cewar Jamila Ibrahim

Jamila Ibrahim ta ce;

“Wani babban soja ya kirani munyi magana fiye da minti 30 akan maganar Seaman Abbas, jikina yayi sanyi sosai wlh…

“Magana ta Allah kar ayi using ƙarfi da viol*ence inba hakan ba za’a ƙara implicating ɗinsa ne, a nemi afuwa kawai a sassauta masa.

“A doka abinda yayi zai iya daɗewa sosai a garƙame ba’aji ɗuriyarsa ba…

“Da farko cikin laifinsa da aka bayyana min ba masallaci yaje ba, Brigade MS zaiyi addressing ɗinsu da safe misalin ƙarfe 10 na safe baizo da wuri ba sai Abbas da abokinsa suka fita basu dawo ba sai da aka gama addressing sauran mutanen…

Karanta Wannan  Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ICPC ta gurfanar da tsohon dan majalisa a kotu bisa zargin satar Naira Miliyan 18 inda kotu ta bayar da belinsa akan Naira miliyan 20

“Da aka hango shi yana zuwa ogansa yace daga ina yake bai amsa ba, akace masa you’re stup!d yace he’s not stup!d dey should address him by his name and rank, nan ne ran ogansa ya ɓaci yace ayi disarming ɗins.

“Sojoji sunje suyi disarming ɗinsa ya ƙi yasa taurin kai yayi cocking bindiga garin a kwace har sai da bindiga ya harba…

“A doka idan kayi cocking bindiga wa oganka a soja tamkar kayi niyyar kisa ne kuma laifinka babba ne babu abinda zai fitar da kai sai anyi maka hukunci mai tsauri…

“Laifi dai shi ya jawa kansa, abinda ya kamata ayi a yanzu shine neman alfarma saboda tausayin iyalansa…

Karanta Wannan  Hotuna: Dandazon Jama’a Sun Halarci Zaman Fadan Sarki Aminu Ado A Yau

“Cikin bayanin da sojan yamun yace ansha aje kotu dashi wajan shara’a sai yasa taurin kai yayi shiru ya ƙi magana, sau uku ana zuwa kotu baya bayani shi yasa ma aka barshi a ɗaure ba’a yanke masa hukuncin da ya dace da shi ba…

“Wannan rubutun nayi sa bisa abinda sojan yace min, ya rage a tsaurara bincike aji gaskiyar lamari a kuma san ta yaya za’a shawo kan lamarin.” In ji Jamila

Menene ra’ayinku?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *