Thursday, June 5
Shadow

Wata Sabuwa: Sanata Natasha Akpoti ta bani Naira Miliyan 200 dan in kalawa Sanata Godswill Akpabio sharri>>Inji Dr. Duru

Rahotanni sun bayyana cewa, Wata farfesa a kasar Amurka me suna Dr. Sandra Duru ta zargi Sanata Natasha Akpoti da nemanta da ta kullawa Sanata Godswill Akpabio sharri tace yana safarar sassan jikin dan Adam.

Dr. Sandra Duru ta bayyana hakane a cikin hirar waya data nada da suka yi ita da Sanata Natasha Akpoti.

Saidai Sanata Natasha Akpoti tace ita bata ma santa ba, dalili kenan da yasa Dr. Sandra Duru ta mikawa jami’an tsaro hirar da suka yi dan su yi bincike akai.

Rahoton yace Sanata Natasha Akpoti ta yi hakanne a yayin da ta ga cewa sharrin da ta ke shirin kullawa kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio na cewa ya nemeta da lalata bai yi nasara ba.

Karanta Wannan  Hotuna:Kalli Yanda aka gano wasu matsafa dake kwakule Kaburbura suna sace sassan jikin mutane a jihar Borno

Matar wadda kuma ‘yar jarida ce tace Sanata Natasha Akpoti bata da wata hujja akan zargin da takewa kakakin majalisar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *