
A yayin da kasar China ke bikin ranar samun ‘yancinta ko kafuwa, shuwagabannin kasashen Korea ta Arewa da Rasha sun halarci taron.
A yayin ganawarsu, an ji Shugaban China, Xi Jingping yana gayawa Putin cewa kamin yanzu ba’a cika samun mutane na kaiwa shekaru 70 ba a Duniya.
Yace amma yanzu dan shekaru 70 ma za’a iya kiransa da jariri.
Putin yace masa da fasahar Biotech, za’a iya canjawa mutum duk wata gaba ta jikinsa data tsufa ko ta lalace wanda hakan zai iya baiwa mutane yin rayuwa ta har abada.
Shugaba Xi na China ya kara da cewa, akwai hasashen mutane zasu iya kaiwa shekaru 150 a Duniya kamin su mutu.