
Rahotanni daga jihar Borno na cewa kungiyar dake ikirarin Jihadi ta ÌŚWÀP ta fadada ayyukan gidan rediyonta inda take yada shirye-shiryenta da yarukan Hausa, Kanuri, da Turanci.
Saidaj ba kaitsaye gidan Rediyon ke aiki ba, suna dauka ne sai a rika turawa kamar yanda ake tura waka ko fim, kamar yanda masanin harkar tsaro, BrantPhilip ya ruwaito.
Ya kuma wallafa Sautin muryar daya daga cikin shirye-shiryen kungiyar da aka nada wanda aka yadashi da Turanci.
Wannan lamari dai ya zowa mutane da mamaki inda da yawa suka rika tunanin yaushe Kungiyar har ta samu nutsuwar yin abubuwa haka?