Monday, December 16
Shadow

Wata Sabuwa: Wasu daga cikin yaran da gwamnatin tarayya ta kama take zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu sun bace an rasa inda suka shiga

Daya daga cikin lauyoyin dake baiwa yaran da gwammatin tarayya ta kama bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu ta hanyar zanga-zanga watau Deji Adeyanju ya bayyana cewa, basu san inda yara 2 daga cikin yaran da gwamnatin tarayyar ta kama auke ba.

Yace yaran biyun ya kamata ace an gurfanar dasu a gaban kotu tare da sauran yara 32 da aka kai kotu ranar Juma’ar data gabata.

Saidai yace zuwa yanzu basu san inda yaran suke ba kuma basu san abinda ya faru dasu ba.

Ya bayyana hakane a wata hira da jaridar Punch ta yi dashi.

Karanta Wannan  T-Pain na nufin wahala ta karamin lokaci, Tinubu zai sake cin zabe a 2027>>Inji Doyin Okupe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *