Hukumar dake kulabda tsayuwar wutar Lantarki a Najeriya ta musanta cewa wutar lantarkin Najeriya ta sake lalacewa.
A sanarwar data fitar ta kafar Twitter, tace a yi watsi da duk wani labari dake cewa wutar lantarkin Najeriya ta sake samun matsala.
A ranar Alhamis ne dai wutar lantarkin ta samu matsala a Najeriya wanda hakan ya jefa kasar cikin duhu.