Saturday, January 11
Shadow

Ya kamata a hukunta Alkalin da yace sake nada Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba daidai bane>>Inji El-Rufai

Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bukaci cewa ya kamata a hukunta Alkalin babbar kotu tarayya da yayi hukuncin cewa sake nada me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin sarki baya kan ka’ida.

El-Rufai wanda abokin Sarki Sanusi II ne ya bayyana hakane a ta shafinsa na sada zumunta inda yake taya Sanusi II murnar tabbatar dashi a matsayin sarkin Kano da kotun daukaka kara tayi.

A baya dai Kotun tarayya ta yi hukuncin cewa, sake nada Sarki Sanusi II baya kan doka amma a yanzu kotun daukaka kara ta soke wancan hukunci.

El-Rufai ya kara da cewa, babbar kotun tarayya bata da hurumin shiga maganar masarauta wadda bata cikin garin Abuja.

Karanta Wannan  ABIN ALFAHRI: Matashi Dan Arewa Na Farko Da Ya Kammala Karatu A Fannin Magungunan Musulunci A Kasar Qatar

An ga dai yanda masoya sarki Sanusi II suka barke da murna bayan da aka tabbatar dashi a matsayin sarkin Kanon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *