
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, yana girmama sojoji kuma bashi da matsala dasu.
Ya bayyana hakane a yayin da ake ci gaba da takaddama akan Tirka-Tirkar data faru tsakaninsa da sojan ruwa, AM. Yerima wanda ya hanashi shiga wani fili a Abuja.
Wike yace ya je wajanne bayan samun rahoton cewa, an ciwa daya daga cikin ma’ikatansa Zarafi, yace shi kuma ba zai bari a rika ciwa ma’aikatan dake karkashinsa zarafi ba.
Yace idan an kaika wajan gadi a matsayin jami’in tsaro aka ce ka harbi mutum, idan ka kashye mutum kana tunanin doka ba zata yi aiki akanka bane?
Yace bashi da matsala da sojoji da yasan yana da matsala da sojoji akwai inda zai je ya warware matsalar.