Friday, December 5
Shadow

Ya kamata jami’o’i masu zaman kansu su shiga ASUU – Shugaban NLC

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero ya yi kira da a janyo jami’o’in Najeriya masu zaman kansu su shiga cikin ƙungiyar ASUU.

Ajaero ya buƙaci ƙungiyar ASUU ta fara tattaunawa da shugabannin jami’o’in na Najeriya domin fahimtar da su buƙatar shiga ƙungiyar domin a gudu tare a tsira tare, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ajaero ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a lokacin da yake jawabi a lokacin da aka tattaunawa da shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna a shirin Toyin Falola.

Shugaban na NLC ya ce “dole a daina cin zarafi tare da yi wa mambobin ASUU,” in ji shi, sannan ya bayyana mamakinsa kan yadda gwamnatin ta gaza wajen tabbatar da alƙawarin da ta sa hannu tun a shekarar 2009.

Karanta Wannan  Ana zargin shugaban bankin First Bank da satar Naira Biliyan 12.3

Ya ce asali an ƙirƙiri ASUU ne domin raba kan NLC, sanan a cewarsa aka hana ASUU zama a ƙarƙashin NLC, matakin da ya ce sun ƙalubalanta a kotu, kuma suka samu nasara.

Ya ƙara da cewa an ƙirƙiri jami’o’i masu zaman kansu ne domin karya lagon ASUU, inda ya ce dole a yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa sun shiga ƙungiyar ta ASUU.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *