
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya kamata mutane su gane cewa, Matsalar tattalin arziki ba a Najeriya bane kadai, Annobace data mamaye kowace kasa a Duniya.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakane a sakonsa na ranar ma’aikata.
Dan haka ya baiwa Ma’aikatan Najeriya hakuri inda yace su co gaba da juriya musamman game da bukatun da suke gabatar masa.
Shugaban yace yana sane da halin matsin rayuwa da yunwa da ‘yan Najeriya musamman ma’aikata ke ciki inda ya sha Alwashin magance wadannan matsaloli.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakane a Eagle Square dake Abuja ta bakin Ministan Kwadago, Muhammad Maigari Dingyadi