Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake hirar soyayya a waya

Hmmm….

Lallai kina son ko kuma kana son ka iya hirar soyayya a waya ko?

To bari dai in fara da cewa, a mafi yawancin lokuta ba a koyata, yanayinkane ke sa budurwa ta soka ko ta kika, ko kuma saurayi ya soki ko ya kiki.

Idan budurwa na sonka, kusan duk abinda kayi daidai ne, hakanan shima saurayi idan yana sonki.

Saidai akwai shawarwari da zan baku da zasu sa ku iya hirar soyayya ta waya.

Yadda ake hirar soyayya a waya

Da farko dai ya kasance kana yawaita kuranta budurwarka.

Ka rika gaya mata irin kyan da take dashi, wane fim ne ake yayi a lokacin, wane labari me dadine ya faru a irin wannan yanayin, wane abune kake tunanin bata sani ba wanda kai ka sani da kuma kake tunanin zai birgeta?

Karanta Wannan  Nasiha ga masoyiyata

Idan zaka gaya mata magana, ka rika hada mata da misali na zahiri wanda ya faru.

Ka rika kawo mata misali da hadisai da Qur’ani, dan mata suna son namiji me ilimi.

Idan ka iya turanci, ka rika gauraya maganarka da turanci.

Kar ka nuna ka kosa da ita.

Idan kaga ta yi wani abu da bai dace ba, ka gyara mata cikin nasiha dan jan hankali.

Ka rika gaya mata irin son da kake mata.

Ka rika gaya mata irin muhimmancin da take dashi a wajenta.

Idan tana magana karka katseta, ka barta ta gama, ka rika girmama ra’ayinta, wanda yayi daidai.

Karanta Wannan  Ya ake farantawa saurayi rai

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *