Wednesday, January 15
Shadow

Yadda ake shinkafa da miya

YADDA AKE SHINKAFA DA MIYA

Kayan hadi :-

Shinkafa
Attaruhu
Albasa
Koren tattasai
Kwai
Plantain
Mangyada

Yadda ake hadawa :-

Dafarko uwargida zaki dora ruwa awuta idanyatafasa saiki zuba shinkafa,idantayi rabin dahuwa,saiki sauke kiwanketa kitace kimayar tukunya kisa ruwa kadan yadda zai turarata,ammafa karyayi yawa don ba ason shinkafar tacabe saiki rage wuta.

Saiki dauko attaruhu kiwanke ki jajjaga, saiki albasa itama ayankata yankan tsaye kiwanketa ki barta akwando tasane,sannan ki dauko koren tattasai kiyankashi ki ajje agefe, saiki dauko plantain ki bare kiyankata,saiki koma kan shinkafarki idanta turara saiki sauke kibarta a tukunyar tadan sha isaka kafin ki zuba a plaks,saiki dauko kasko ko tukunya kizuba mai kisoya plantain dinnan ki ajje agefe, sannan ki dauko tukunyar dazaki yi miyar ki aciki kizuba mai idan yayi zafi saiki sa albasa idantayi brown saiki zuba attaruhun dakika jajjaga da albasa da koren tattasan saiki juya zaki iyasa farin maggi kadan idan kina so,saiki sa maggi mai star da sauran kalolin maggin da kikeso,

Karanta Wannan  Da Duminsa: Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan dambarwar Sarautar Kano

kisa seasoning mai dadi saiki zuba citta da kanunfari kadan wanda dama already anaso mace ta dake citta,kanunfari,masoro,gyadar yarabawa mai kamshi da tafurnuwa tadake abinta tazuba aroba idan zaki jar miya ko jallop saikisa, to bayankinzuba saiki juya sosai idan miyar ta soyu saiki rufe kirage wutar kibarshi zuwa minti daya dakinbude zakiga miyar takwanta kayan miyan sunhade jikinsu saiki sauke ki dora ruwa kidafa kwai idan yahuce saiki bareshi kwashe shinkafarki saiki zuba a plet saiki sa miyar agefe kizuba plantain dinma agefe, sannan kisa kwanki agefe kidanyi musu decoration maikyau shikenan girkinki yakammala saici.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *