Monday, December 9
Shadow

‘Yansanda sun kama masu gàrkùwà da mutane a Kano

‘Yansanda a jihar Kano sun kama masu laifi gida 82. An kamasu ne tsakanin Nov. 1 zuwa Nov. 14.

Wanda aka kama din ana zarginsu da aikata laifukan kwacen waya, garkuwa da mutane da safarar kwaya.

Kakakin ‘yansandan jihar, Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana haka a hedikwatar ‘yansandan jihar dake Bompai Kano.

Ya bayyana cewa sun samu wannan nasara ne bayan wasu dabaru da suka fito dasu na kama masu laifi.

Yace sun kwace makaman Bindiga AK 47 guda daya da bindigu kirar gida guda 3 da adduna da wukake guda 30 sai miyagun gwayoyi da sauransu.

Ya bayar da tabbacin ci gaba da kokarin kawo zaman lafiya a jihar da yaki da aikata miyagun laifuka.

Karanta Wannan  WATA SABUWA:Ku Shirya Fuskańtar Wahalar Mań Fètur Fiye Da Wańda Ake Ciki A Yanzu, Sakon Kamfanin NNPCL Ga 'Yan Nąjeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *