Monday, December 16
Shadow

Yadda ake tsara budurwa farkon haduwa

Farkon haduwarka da budurwa yana da muhimmanci, musamman saboda duk abinda ya faru a tsakaninku shine zai zama ya darsu a zuciyarta zata rika Tunawa dashi.

Ita soyayya makauniyace abinda zai ja hankalin waccen macen ba lallai shine zai ja hankalin dayar macen ba amma a al’adance mata nason abu me daukar hankali da kalamai masu sanyaya zuciya da kuma abu me sa nishadi.

Dan haka a shawarce haduwarka ta farko da budurwa ya zamana ka kure adakata, watau ka ci kwalliya, duk da yake haduwar zata iya zama accidental watau ku duka babu wanda ya shirya.

Amma ka sani fita da kwalliya da daukar wanka me kyau yana kara daukar hankalin ‘yan mata, bari na dan baka wani labari gajere.

Akwai sanda na shirya haka kawai na fita yawo da yamma, shaddata sabuwace takalmi na me kyaune sosai, gashi inata kanshi malam.

Wallahi in takaice maka zance saida wata budurwa ta kyasa, ta rika matsowa kusa dani muna zaune a Adaidaita sahu watau Keke Napep, kai saita ta rika tabani tana son in mata magana, ni kuma a lokacin Allah yasan bata min ba, bawai bata da kyau bane, kawai kibarta ce ta min yawa gaskiya dan ni ina son mace siririya.

Karanta Wannan  Kalaman soyayya masu dadin gaske

Saidai kuma wani ikon Allah, wallahi har yau na kasa mantawa da wannan baiwar Allah, ina sauka daga keke Napep din na biyashi ya tafi wallahi naji wata soyayyarta kawai ta lullubeni, muna tare da abokinane sai da na bashi kudin mashin ya bisu amma bai gano inda suka shiga ba, nafi wata inata tunanin wannan baiwar Allah, kai saboda zautuwar soyayya sai da na rika komawa wajan dana sauka na rika tsayawa ko zan ganta amma ban ganta ba.

Abinda nake son ka dauka a wannan gajeren labarin shine shigarka zata taimaka maka sosai wajan yin nasarar samun mace musamman a karin farko.

Karanta Wannan  Hirar soyayya masu dadi

Kuma na sha samun irin wannan cases din inda ban wa mace magana ba kawai kaga muna ta kallon kallo na soyayya, saboda ni mutum ne me son kwalliya.

Abu na gaba shine kalamai masu dadi.

Idan ka ga wadda kake so, ka garzaya ka mata sallama, zata iya amsawa zata iya shareka, kada wannan ya dameka, ka fadi wani abu da zai sata dariya ko zai ja hankalinta, kamar tambaya nake, ko an aikoni wajenki ne, watau zuciyarka ta aikeka, da dai sauransu.

Ya danganta da Confidence dinka da kuma irin kimarka, kana iya mata sallama kai tsaye kace mata dan Allah ta taimaka maka da lambarta.

Saidai ka kiyaye, duk maganar da zaku yi kada ka tsawaitata, musamman idan tana tafiyane, saboda baka san uzurinta ba.

Kana kuma iya janta da hira akan wani abu da ka ganta dashi.

Karanta Wannan  Menene soyayya

Misali akwai wata budurwa dana taba yi itama abin hawa ya taba hadamu.

Na ganta da littafi ta dawo daga wajan bikine, da wannan na zolayeta muka fara hira sosai da muka sauka karbar lambarta be min wahala ba.

Ban cika son idan ina tuka mota in yi budurwa ba, nafi son in yi budurwa idan ina tafiya a kasa ko naje siyayya ko akan abin hawa na haya,ko idan na fita motsa jiki da safe.

Akwai wanda na sani, Shi budurwa idan yana sonta,karin farko kudi yake dauka ya bata masu dan kauri. Amma illar wannan shine ba lallai ta soka dan Allah ba, saidai da wuya ka samu wadda zata ce bata sonka.

Don haka zabi ya rage gareka.

Ka zama dan gaye,ko ka iya hira me ban dariya ko me daukar hankali cikin kankanin lokaci ko ka yi amfani da kudi.

Wanne kafi so?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *