Monday, May 12
Shadow

Yajin aikin ma’aikatan NIMET ya hana wasu jirage tashi a Najeriya

Harkokin sufurin jiragen sama na fuskantar cikas a filayen tashi da saukar jiragen sama na cikin gida yayin da ma’aikatan hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ke gudanar da yajin aikin kan rashin ingancin yanayin aiki.

Yajin aikin da ya yi kwana biyu yana gudana ya haifar da maƙalewar fasinjoji a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja, da filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas da sauran filayen jiragen sama da ke faɗin ƙasar.

Kamfanin sufurin jiragen sama mafi girma a Najeriya, Air Peace ya sanar da dakatar da ayyukansa sakamakon yajin aikin.

Kamfanin ya sanar da cewa ya yanke shawarar dakatar da sufurin jiragensa ne saboda kiyaye rayukan fasinjojinsa.

Karanta Wannan  Yunwa da Talauci ne ke jawo matsalar tsaro a Najeriya>>Shugaba Tinubu

Kafar yaɗa labarai ta Channels ta rawaito cewa a filin jirgin saman Legas, kamfanin XEJET da Aero Contractors, da Ibom Air sun yi aiki kamar yadda aka tsara a ranar Laraba, yayin da Air Peace bai yi aiki ba.

Domin shawo kan lamarin, ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya shirya ganawa da wakilan mambobin ƙungiyar ma’akatan hukumar NiMet masu zanga-zangar.

An shirya gudanar da taron a yau (Alhamis).

Ma’aikatan NiMet sun rufe cibiyoyin kula da yanayi a filayen tashi da saukar jiragen sama kuma sun janye duk ayyukan kula yanayi a faɗin ƙasar a ranar Laraba yayin da suke neman a biya musu buƙatunsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *