Rahotanni sun bayyana cewa tituna da ma’aikatu babu mutane sosai a Abuja saboda yajin aikin da kungiyar kwadago ta NLC ta tsunduma a yau, Litinin.
Rahoton yace babbar kotun kasa, ma’aikatar mata ta tarayya, da sauransu duk an kulle saboda yajin aikin.
Kungiyar NLC dai ta shiga yajin aikinne saboda nuna rashin jin dadin Naira dubu 60 da gwamnatin tarayya tace zata biyasu a matsayin mafi karancin Albashi.
[…] A Abuja ma dai haka lamarin yake inda NLC ta kulle guraren aiki da yawa ta hana ma’ikata shiga. […]