Wednesday, January 15
Shadow

‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan yadda ya kasa sarrafa gine-ginen tsaro a jihar.

Lawal ya ce ba shi da iko a kan shugabannin hukumomin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa suna karbar umarni daga manyansu.

Da yake jawabi yayin wani taron birnin tarayya na bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya karo na 25 a Abuja ranar Laraba, gwamnan ya yi tir da ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

A cewar Lawal: “Da sunan, ni ne babban jami’in tsaro na jihata amma idan ana maganar umarni da iko, ba ni da iko a kan duk wani jami’in tsaro na soja, ko ‘yan sanda ko na Civil Defence.

Karanta Wannan  KUNCIN RAYUWA: An Kama Baŕawoñ Alĺuñañ Makabarta A Kano

“Suna karbar umarninsu daga manyansu ba daga gwamnoni ba. Ba mu da wannan iko, ina fata muna da, da ya kasance wani labari na daban. “

Ya ce matsalar tsaro ba ta gyaru a jihar ba sakamakon katsalandan da ya bayyana a matsayin siyasa.

A cewar gwamnan, hukumomin tsaro na da dukkan abin da ya kamata na murkushe masu aikata laifuka a fadin kasar nan, idan har suna da ra’ayin siyasa

Daga: Abbas Yakubu Yaura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *