
‘Yan Bindiga a daren ranar Alhamis sun tare wata Motar Bas inda suka sace mutanen cikinta su duka.
Motar dai na tafiyane akan Titin Malunfashi zuwa Funtua.
Rahoton yace lamarin ya farune a daidai kauyen Burdugau kamar yanda me amfani da kafar X, Bakatsine ya bayyana.
Saidai zuwa yanzu babu wata sanarwa daga hukumomi game da lamarin.