
A yayin da rikicin kasar Israyla da Falasdiynawa yasa farashin danyen man fetur a kasuwannin Duniya ya tashi zuwa dala $74 kan kowace ganga.
‘Yan kasuwar man fetur a Najeriya sun kara farashin man fetur din nasu a gidajen mai daban-daban.
Misali gidan man Aiteo ya kara farashin man fetur dinsa zuwa Naira 840 kan kowace lita daga Naira 835 da ake sayar da ita a baya.
Hakanan gidan man Pinnacle sun kara farashin man fetur dinsu zuwa 845 akan kowace lita maimakon Naira 829 da suke sayarwa a baya.
Dangote kuwa ya kara farashin man nasa ne zuwa Naira 840 kan kowacw lita maimakon 830 da yake sayarwa a baya.
Ana tsammanin farashin man fetur din zai ci gaba da tashi a kasuwannin Duniya saboda rashin tabbas a kasuwar.