
‘Yan majalisar jihar Rivers 2 sun bayyana janyewa daga yunkurin tsige gwamnan jihar, Simi Fubara.
‘Yan majalisar sun ce sun dauki wannan matakine biyo bayan kiraye-kirayen dattawa a ciki da wajen jihar ta Rivers su canja matsayarsu.
Sun ce duk da gwamnan yayi laifi na karya dokar kundin tsarin mulki amma suna kira ga abokan aikinsu da su duba au sassauta a janye wannan matsaya.