
Rahotanni daga jihar Yobe na cewa mahara wanda ake tsammanin mayakan kungiyar Bòkò Hàràm ne sun kai hari sansanin sojoji na 27 dake Gujba karamar hukumar Buni Yadi ta jihar Yobe inda suka kashe sojoji 4.
Hakanan maharan sun lalata motocin yakin sojojin.
Hakan na zuwane kasa da awanni 24 bayan da Gwamnonin yankin Arewa maso gabas suka yi taro a Damaturu dan samar da tsaro a yankinsu.
Daya daga cikin sojojin wanda ya tsira daga harin yace ‘yan Bindigar sun afka musu ne da misalin karfe 2 na dare ranar Asabar.
Yace mamayarsu maharan suka yi amma an yi musayar wuta inda sojoji 4 suka mutu kuma suma sun kashewa ‘yan ta’addar mutane sosai.
Hedikwatar tsaro ta tabbatar da harin amma bata bayar da cikakken bayani ko an samu wadanda suka mutu ba ko a’a