Tuesday, March 17
Shadow

Yanda Sanata Akpabio Ya taba rike hannuna a gaban mijina>>Sanata Natasha Akpoti

Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi ta bayar da labarin yanda Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya taba rike hannunta a gaban mijinta.

Tace a lokacin sun je taya Akpabio murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne inda mijinta ya rakata.

Tace Sanata Akpabio ya kama hannunta ya jata ya rika nuna mata gidansa yayin da mijinta ke binsu a baya.

Tace abin ya damu mijinta a lokacin wanda daga nan ya rika cewa ba zata rika yin tafiya ita kadai ba.

Karanta Wannan  Hotuna: Yadda dan gidan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya kammala digiri na biyu a Jami'ar kasar Ingila, Inda ya karanci fannin shari'a. Ministan ne ya wallafa hakan a shafinsa na X, inda yake alfahari da hakan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *