‘Yansanda sun kashe daya daga cikin masu tursasawa mutane zama a gida.
An yi bata kashine tsakanin ‘yansandan da mutanen wanda aka kashe daya, sauran suka tsere.
Hukumar ‘yansandan tace lamarin ya farune ranar 30 ga watan Mayu.
Kuma ta kwace Bindiga kirar gida daga hannun daya daga cikin ‘yan ta’addan inda sauran suka tsere, kamar yanda kakakin ‘yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga ya tabbatar.