Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira Dubu sittin da biyu a matsayin sabon tayinafi karancin Albashi ga kungiyar Kwadago.
Hakanan Sabon rahoton ya bayyana cewa, kungiyar kwadago ta NLC ta sauko daga matsayin ta na cewa gwamnati ta biyata Naira dubu dari hudu da chasa’in da hudu(494,000) inda a yanzu tace a biyata Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000).
Tuni dai kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta amince da tayin na gwamnatin tarayya watau dubu 62,000.