DSS Ta Kama Mahdi Shehu Saboda yada Bidiyon sojojin Faransa.
Hukumar tsaro ta farin kaya ta (DSS) ta kama Mahdi Shehu, mai fafutuka kuma mai sharhi kan al’amuran siyasa daga Kaduna.
An Kama shi ne biyo bayan zargin da ake yi masa na yaɗa bidiyon sojojin Faransa a shafinsa na X.
A cewar rahotanni, bidiyon ya nuna Shehu yana ikirarin cewa gwamnatin Najeriya tana shirin kafa sansanin sojojin Faransa a yankin Arewa maso Yamma, ikirarin da aka musanta. Mahdi yana hannun DSS a Kaduna, kuma akwai yiwuwar a gurfanar da shi a gaban kotu nan ba da jimawa ba.
Hukumar DSS ta bayyana cewa sun tattauna da Mahdi kan rashin ingancin bayanan bidiyon kafin kama shi, amma tattaunawar ba ta kai ga nasara ba. Duk da haka, an umarci jami’an tsaro su mutunta haƙƙinsa yayin tsare shi.