Kungiyar Real Madrid ta lashe kofi na 15 bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 2-0 a wasan karshe da suka buga a filin wasa na Wembley.
Dani Carvajal da Vinicius Jr ne suka ci kwallayen 2.
Tsohon dan wasan Real Madrid din kuma kocinta, Zinedine Zidane ne ya kai kofin filin:
Kungiyar Borussia Dortmund ta gayyaci Jurgen Klupp ya kalli wasansu. Shine dai ya kaisu wasan karshe na gasar da suka buga a shekarar 2013.
Mahaifi da mahaifiyar Jude Bellingham da dan uwansa sun je kallon wasan.
Hakana mawakin Amurka Jay Z ma ya je kallon wasan:
An samu wani da yayi kutse a cikin filin inda ya je ya dauki hoto da Vinicius.