Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kafa wani kwamiti na musamman dan binciken zargin da akewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kan satar Naira Biliyan 423.
Za’a binciki tsohon gwamnan ne tare da wasu manyan da suka yi aiki tare da shi a gwamnatinsa.
Nan gaba kadan ake sa ran EFCC din zasu gayyaci El-Rufai dan binciken sa.
Hukumar ta EFCC tace sun karbi korafi dake bukatar a bincike tsohon gwamnan na jihar Kaduna.
za a bincike gwamnan ne tare da sauran mukarrabansa da suka yi aiki tare dashi tsakanin shekarau takwas daya yi akan karagar mulki.
Cikin wadanda za a bincika hadda ma’aikatan KADRIS KADRA amma banda injiniya Amina jafar Ladan wadda aikin wata daya kacal tayi.