Wednesday, January 15
Shadow

Yanzu-Yanzu:Kasar Faransa ta hana kasar Yahudawan Israela zuwa bikin nuna makamai saboda kisan Falas-dinawa

A karin farko, Kasar Faransa ta zama kasar Turai ta farko data kakabawa kasar Israela takunkumi kan kisan kiyashin da takewa falasdinawa.

Faransar ta hana kasar Israela hakartar bikin nuna makamai da za’a yi ranar 17 zuwa 21 ga watan Yuli.

Bikin dai shine bikin nuna ko kuma bajakolin makamai mafi girma a Duniya wanda aka sakawa sunan Eurosatory 2024.

Wannan mataki na zuwane bayan da kasar Israela ta ki bin umarnin kotun Duniya na daina kashe Falasdinawa.

Hakanan kasashen Duniya da yawa na ta Allah wadai da kasar kan kisan da takewa Falas-dinawan.

Sannan kuma wannan mataki zai iya zama gargadi ga kasar ta Israela ta canja salo ko kuma akwai yiyuwar wasu sauran kasashen Turawa suma su saka mata takunkumo.

Karanta Wannan  Tauraruwar Fina-Finan kasar Amurka, Angelina Jolie ta yi Allah wadai da shuwagabannin kasashen Duniya saboda kyalewa da suka yi anawa Falas-dinawa kisan kiyashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *