Friday, December 5
Shadow

Yaro mai shekaru 11 ya mùtù bayan ya fado daga bishiyar mangwaro

Wani yaro dan shekara 11 mai suna Joshua Samson ya mutu bayan ya fado daga bishiyar mangwaro a kauyen Bugakwo da ke karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin Bugakwo mai suna Danjuma, ya shaidawa DAILY TRUST cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, a lokacin da marigayin ya hau bishiyar mangwaro don ya tsinka.

Ya ce yaron ya hau bishiyar mangwaron ne domin ya tsinko mangwaro, amma sai ya zame daga kan reshen ya fado kasa.

Ya ce daya daga cikin yaran da suka je diban mangwaron ne ya ruga gida yana kuka ya kai rahoto ga iyayen marigayin, inda suka garzaya da shi asibiti.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Cikin darennan Bàm ya fashe a gidan yarin Maiduguri jihar Borno

Ya ce yaron ya mutu ne bayan kansa ya bugu a kan dutse a karkashin bishiyar mangwaron, inda ya ce an binne yaron.

“Ma’aikatan lafiya a cibiyar lafiya ta Kwaku sun tabbatar da mutuwarsa saboda munanan raunukan da ya samu a kai,” in ji shi.

Danjuma ya ce iyayen marigayin ba su kai rahoton faruwar lamarin ga jami’an tsaro ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *