Wednesday, April 8
Shadow

Yaudarar mu ADC suke, ba zasu iya tsinana komai ba ko da sun samu mulki>>Inji Datti Baba Ahmad

Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa, Jam’iyyar ADC yaudarar talakawa kawai suke ko sun samu mulki babu wani ci gaba da zasu iya kawowa.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV ranar Juma’a.

Datti na wannan maganar ne duk da cewa, Peter Obi wanda suka yi takara tare a yanzu yana jam’iyyar ADC.

Datti dai yace, yana fatan Peter Obi zai koma jam’iyyar Labour party yayi takara acan.

Da aka tambayeshi ko zai sake yiwa Peter Obi takarar mataimakin shugaban kasa? Datti Baba Ahmad ya ce Eh.

Karanta Wannan  Mutum Biyu sun taba nunawa mamana Bidiyon wakokin da nake yi, na duresu, saboda me yasa zasu nuna mata salon su tayar mata da hawan jini? Inji Soja Boy me waka yana tabawa da Rhunghumar mata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *