Saturday, March 15
Shadow

Yawanci masu sharhi akan dakatar da sanata Natasha Akpoti jahilaine, kamar wanda ba musulmi bane yace zai fassara Qur’ani>>Sanata Godswill Akpabio

Kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya gargadi ‘yan Najeriya da su daina tsoma baki akan abinda basu da ilimi akansa.

Ya jawo hankalin ‘yan Najeriya da cewa, su fahimci dokokin majalisar kamin su tsoma baki akan harkokinta.

Ya bayyana hakane a yayin da wasu kungiya daga yankinsa na Niger Delta suka kai masa ziyara.

Hakan na zuwane a yayin da ake ta bayyana ra’ayoyi mabanbanta game da dambarwarsa da Sanata Natasha Akpoti.

Ya bayyana cewa masu sharhi akan al’amuran majalisar ba tare da sanin dokokinsu ba kamar me maganin gargajiyane dake son fassara Baibul ko wanda ba Musulmi ba yayi kokarin fassara Qur’ani.

Karanta Wannan  Hotuna: Jami'an tsaro sun kashe masu garkuwa da mutane 3 a Kaduna

Akpabio yace kujerar da yake kai rabon yankinsu na Niger Delta da samunta tun shekaru 46 da suka gabata yace kuma ba dan shi bane yake kan kujerar, yana wakiltar yankin Niger Delta ne wanda ke da matukar Tasiri wajan karfafa tattakin arzikin Najeriya dan haka ba zai yi wasa da wannan damar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *