
Shekara biyu bayan ƙaddamar da aikin haƙo ɗanyen man fetur a iyakar jihohin Bauchi da Gombe – wanda tun daga wancan lokaci ba a ci gaba da aikin ba – a yanzu sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya Bayo Ojulari ya fada wa BBC cewa za a koma kan aikin.
Aikin da aka ƙaddamar a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata, ya sanya al’ummar arewacin ƙasar sun fara kyakkyawar fatan cewa yankin zai bi sahun wasu yankunan ƙasar da ke samar da man fetur wanda tattalin arzikin ƙasar ya dogara a kai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, wadda ke da alaƙa tashin farashin man fetur a sanadiyar cire tallafin da gwamnati ke bayarwa a bangaren.
Tun a jawabin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na farko bayan shan rantsuwar kama mulki ne ya sanar da cire tallafin man fetur.
Tun daga lokacin ne farashin man fetur ɗin ya fara tashi, wanda kamar yadda aka saba, farashin kayayyaki da kuɗin sufuri da sauran abubuwa suma suka tashi a faɗin ƙasar.
Shi dai tallafin man fetur ɗin nan wasu kuɗaɗe ne da gwamnatin tarayya ke fitarwa domin biyan wani ɓangare na kuɗin da ake kashewa wajen sayowa da shigo da tataccen man fetur daga kasuwannin duniya zuwa Najeriya tare da sufurinsa zuwa jihohi domin ƴan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.
Hakan ya sa ƴan arewacin Najeriya suka shiga murna da farin cikin ganin za a fara haƙo ɗanyen man daga yankinsu, wanda hakan zai sa su same shi ba tare da wahalar sufuri ba.