Ma’aikatar ayyuka ta ware Naira Biliyan 4 dan kashesu wajan ginawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu filin da zai rika sauka da karamin jirginsa.
Tuni ma’aikatar ta saka wannan aiki na gina filin saukar jirgin a cikin kasafin kudinta na shekarar 2025.
Wasu dai sun soki hakan da cewa bata kudin ‘yan kasa ne musamman ganin yanda ‘yan Najeriya da dama ke cikin halin ji ‘yasu inda ake ganin da an saka kudin a wani fanni da sun taimaka sosai.