
A yau, Alhamis, za’a yi zaman majalisar zartaswa dan karrama tsohon shugaba kasa, Marigayi Muhammadu Buhari wanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai jagoranta.
Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Facebook.
A ranar Lahadin data gabata ne dai tsohon shugaban kasar ya rasu a landan yana da shekaru 82.
An kuma binneshi a mahaifarsa Daura.