Firaiministan kasar Israel, Benjamin Netanyahu na fama da cutar yoyon fitsari inda za’a yi masa tiyata a yau, Lahadi dan samun sauki.
Ofishinsa ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Hakan na zuwane yayin da kasar ke ci gaba da yakar Kungiyar Hàmàs.
A baya dai dama an taba yi masa tiyatar Haniya.