Mun sha kwana ba mu ci abinci ba… wata magana daga bakin Zainab Muhammad, wadda aka fi sani da Mrs. Zanel, yayin da take ba mu labarin wasu daga cikin ƙalubalen rayuwar da ta fuskanta kafin ta kai matsayin da take a yau. Daga rayuwar ƙalubale zuwa zama ɗaya daga cikin fitattun masu ɗinkin zamani na maza a birnin Abuja, Mrs. Zanel ta bayyana mana yadda jajircewa, haƙuri da taimakon Allah suka sauya mata tafiyar rayuwa. A cikin wannan hira ta musamman a Rayuwata Talk Show, za ku ji labarin mutumin da ya taimaka mata wajen biyan kuɗin makaranta, yadda ta fara sana’a tun bayan zuwanta Abuja domin NYSC, da kuma yadda daga ƙarshe ta gina nata Company kuma ta zama sananniya a fannin fashion. Wannan labari nata cike yake da darussa ga duk wanda yake cikin ƙalubale kuma yake da burin canza rayuwarsa. Ku kalli cikakkiyar hirar yanzu domin jin wannan labari mai cike da ƙoƙari, haƙuri, taimako da ikon Allah. 🎙️ Rayuwata Talk Show — Telling Real Life Stories Powered by Tubless Media Concept