
Wani zaki da Balarabe a garin Najaf dake kudancin kasar Iraqi ya siyo dan ya rika wasa dashi, ya kashe me gidan nasa kwanki kadan bayan siyoshi.
Bayan ya kasheshi, ya kuma cinye kusan duka gawar me gidan nasa.
Lamarin ya faru ranar 8 ga watan Mayu.
Kakakin ‘yansandan yankin Najab, Mufid Tahir, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sai da aka kashe zakin saboda yaki yadda ya daina cin gawar me gidan nasa.
Me gidan Aqil Fakhr al-Din na da shekaru 50 kuma an bayyana cewa ya dade yana ajiye zaki a gidansa.