Friday, January 23
Shadow

Zamu rama kashe mana sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi, zamu tabbatar mun yi maganinsu>>Inji Hukumar sojojin Najeriya

Hukumar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan sojoji 5 da kungiyar IPOB suka yi.

Hukumar tace an kashe sojojin ne dake rundunar Operation UDO KA da aka kai Obikabia.

Tace akwai kuma farar hula 6 da suma aka kashe a yayin harin.

Kakakin hedikwatar tsaro, Majo Janar Edward ne ya bayyana hakan inda yace zasu tabbatar sun rama wannan kisan da aka musu.

Hukumar sojin tace maharan sun je wajanne a motocin Prado 3 dake da bakin gilashi sannan akwai wasu kuma a yankin da suma suka farwa sojojin.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Yanda 'yan B0k0 Hqrqm suka yanka mutane 7 a Bassa da Erena dake jihar Naija

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *